Shugaban kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu ya ce gwamnatin tarayya ta sani cewa bata isa ta sake kama shi ba muddun yana yankin Kudu Maso Gabas, idan kuma an matsa to wanda ya zo don haka za a dauki gawarsa ne.
” Wasu dakikai marasa hankali sunce za su sake kamani. Idan sun isa su zo gani su kamani. Su zo gani duk wanda ya ko shigo wannan yankin namu na Biafra kuma ya fita da ransa ba nan ya shigo ba. Kuje ku Gaya musu na ce haka.”
” Ku gaya ma Buhari cewa ina nan a garin Aba kuma duk wanda ya ce zai zo ya kama ni a garin Aba to zai mutu a nan. Ba zan gudu ko ina ba wannan karon ina nan amma idan an isa azo a kama ni.”
Nnamdi Kanu ya ce suna nan akan bakan su na neman kasar Biafra kuma ba za su dai na ba har sai sun samu kasarmu.
” Ku manta wadannan maganganun banzan da suke fadi akan mu. Babu wanda ya isa ya hana mu neman kasarmu na Biafra. Idan an isa azo a hana mu mu gani.”
Source: Premium Hausa
Title :
Ku Fada Wa Buhari Inanan A Aba Kuma Ba wanda Ya Isa Yakamani-Nnamdi Kanu
Description : Shugaban kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu ya ce gwamnatin tarayya ta sani cewa bata isa ta sake kama shi ba mudd...
Rating :
5