Wata kotun tarayya da ke birnin Laegas na Najeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar N7.6bn, kudin da ake zargin tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke ta sace.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC ce ta gano kudin a wani banki, inda ta yi zargin cewa tsohuwar ministar ta same su ne ta hanyar da bata dace ba.
EFCC ta ce an ajiye kudin ne a asussa da dama.
Alkalin kotun mai shari'a Abdulaziz Anka ya yanke hukuncin ne bayan da EFCC ta nemi kotun ta mallakawa gwamnati kudin dindindin.
A farkon watan nan ma wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Najeriya kaddarorin tsohuwar ministar man da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.
Kotun ta mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Ms Diezani da ke yankin Banana Island da ke Lagos, wanda kudinsa ya kai $37.5m, kimanin naira biliyan 13.
Haka zalika, mai shari'a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin Najeriya naira sama da naira miliyan 84 da kuma sama da dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.
A kwanan baya dai kotun ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kadarorin na wucen gadi, bayan hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta nemi kotun ta mallawaka wa gwamnati kadarorin.
Bayan haka ne dai kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a kafafen yada labarai, domin duk wanda ke da wani dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na din-din-din ba ya kawo dalilinsa gaban kotun.
A watan Afrilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai naira miliyan 593 daga hannun tsohuwar ministar.
Ana zargin ta da sace wa da kuma yin facaka da kudin kasar a lokacin da take ministar man, ko da yake ta sha musanta zargin.
A watan Fabrairun 2017 ma, wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar man, Diezani Allison-Madueke
Source: BBC Hausa
Title :
Kotu Ta Mallakawa Gwamnati N7.6bn Na Diezani
Description : Wata kotun tarayya da ke birnin Laegas na Najeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar N7.6bn, kudin da ake zargin tsohuwar ministar mai Diezani A...
Rating :
5