Koriya Ta Arewa ta harba wani makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan, wani al'amari da Firai Ministan Jaan Shinzo Abe ya ce hakan wata babbar barazana ce da ba a taba samun irin ta ba.
An harba makamin ne a ranar Talata da sassafe agogon Koriya, wanda ya bi ta tsibirin Hokkaido kafin daga bisani ya fada cikin teku.
Ana sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa don mayar da martani kan lamarin.
A baya-bayan nan ne Koriya Ta Arewa ta aiwatar da wasu gwaje-gwajen makamai masu linzami, amma wannan ne karo na farko da ta harba mummunan makami mai linzami ya bi ta samaniyar Japan.
A karo biyu a baya da rokokinta suka bi ta samaniyar Japan a shekarar 1998 da ta 2009, Koriya Ta Arewa ta ce tana kaddamar da tauraron dan adam ne ba makamai ba ne.
Wakilin BBC a Tokyo Rupert Wingfield-Hayes, ya ce ga alama wannan makami na farko da aka harba wanda ka iya daukar makamin nukiliya.
An umarci mazauna kasar su nemi mafaka
Rundunar sojin Koriya Ta Kudu ta ce an harba makami mai linzamin ne ta gabas kafin karfe 6:00 na safe, wanda ya yi daidai da karfe 9:00 na daren Litinin agogon GMT, daga Pyongyang, babban birnin kasar, wanda ba a cika samun hakan ba.
Wani sharhi da aka yi na farko ya nuna yadda harbin makamin ya kasance:
Kwanan nan ne dakarun Amurka da na Japan suka kammala wani atisaye na hadin gwiwa a Hokkaido yayin da ake ci gaba da wani atisayen na dubun-dubatar dakarun Koriya Ta Kudu da Amurka a Koriya Ta Kudun.
Koriya Ta Arewa na kallon wannan atisaye na hadin gwiwa da ya hada da sojojin Amurka a matsayin wata tsokana, inda suke ganinsa a wani yunkuri na kai mata hari.
Shugaban kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-in, ya bayar da umarnin dakarun kasar su fito su yi gagarumin atisaye don mayar da martani ga harin. Jiragen yakin Koriya Ta Kudu sun yi ta atisayen harba bama-bamai a ranar Talata.
Mr Abe ya ce ya yi magana da Shugaba Donald Trump kuma duk su biyun sun amince a kara matsa wa Koriyta Ta Arewa lamba.
Sai dai cibiyar tsaro ta Amurka ta ce wannan hari ba barazana ce ga kasar ba, amma sojoji na aiki don tattara bayanan sirri game da harin.
China ta yi gargadi cewa tashin hankali ya kai kololuwa a yankin Koriya, amma ta ce Amurka da Koriya Ta Kudu ne abin zargi. Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron China Hua Chunying, ta soki kasashen biyun da ci gaba da atisayen sojin da suke yi wanda ke zama kamar matsin lamba ga Koriya Ta Arewa.
Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov, ya ce, kasar ta damu matuka a kan yiwuwar tabarbarwar da lamarin zai yi, amma ya ce atisayen da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu ke yi yana kara harzuka Koriya Ta Arewa.
Source: BBC Hausa
Title :
Koriya Ta Harba Makami Mai Linzami Ta Saman Japan
Description : Koriya Ta Arewa ta harba wani makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan, wani al'amari da Firai Ministan Jaan Shinzo Abe ya ce haka...
Rating :
5