Wani kwamandan dakarun ruwan Amurka, ya tabbatar da cewa Korea ta Arewa, ta yi gwajin wasu makamai masu linzami, wadanda suke tafiyar gajeran zango a jiya Juma’a, amma kuma, makaman ba su kai ga inda aka yi niyyar su kai ba.
Kakakin rundunar sojin Amurka a yankin Tekun Pacific, ya ce makamai masu linzami uku Korea ta arewan ta harba, inda ta rika ba da tazarar kusan minti goma-goma a tsakaninsu.
Ya kuma kara da cewa, babu ko daya daga cikin makaman da zai yi barazana ga yankin arewacin Amurka ko kuma Guam, wanda shi ne yanki mallakar Amurka mafi kusa da Korea ta Arewan.
Tun da farko, dakarun Korea ta Kudu, sun sanar da cewa makwabciyarta ta Arewa, ta harba wasu makamai masu linzami da dama daga Lardin Gangwon, wadanda suka ce watakila wani fanni ne na atisayen da sojojin kasar ke yi.
Source: VOA Hausa
Title :
Korea Ta Arewa Tayi Gwajin Makamai Masu Linzami
Description : Wani kwamandan dakarun ruwan Amurka, ya tabbatar da cewa Korea ta Arewa, ta yi gwajin wasu makamai masu linzami, wadanda suke tafiyar gajera...
Rating :
5