Shekaru uku kenan da 'ya'yan masarautar Saudiyya su 3, da suke zaune a kasashen turai suka yi batan dabo, kuma dukkansu na sukar lamirin gwamnatin kasar. Akwai alamun dukkan ukun an tasa keyarsu gida Saudiyya, kuma tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsu ba.
Da sanyin wata safiya a ranar 12/06/2003, aka tasa keyar daya daga cikin Yariman wajen birnin Geneva.
Sunansa Sultan bin Turki yarima Abdulaziz bin Fahd, ya gayyace shi cin abincin safe
Abdulaziz ya roki Sultan ya koma gida Saudiyya, inda ya shaida masa za a magance kace-nacen da ake yi kan sukar da ya ke yiwa shugabannin kasar.
Amma sai Sultan ya ki amincewa da hakan, a wannan lokacin ne yarima Abdul'aziz ya tashi daga inda suke zaune dauke da wayar salula da aka kira shi.
Jim kadan ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya Sheikh Saleh al-Sheikh da suke tare a dakin cin abincin shi ma ya fita, bayan dan lokaci sai wasu mutane sanye da wani bakin kyalle da suka rufe fuskokinsu da shi, su ka shigo dakin, suka kuma lakadawa Sultan dan karen duka, aka kuma soka ma sa wata allura a wuyansa.
Sultan ya shiga wani yanayi na dimuwa da gushewar hankali, a hakan aka dauke shi har filin jirgin sama na Geneva, aka sanya shi a cikin wani jirgi da daman ya na zaman jiran su ne.
Source:BBC Hausa
Title :
Ko Shin Masarautar Saudiyya Nada Hanu A Bacin 'Ya'yanta
Description : Shekaru uku kenan da 'ya'yan masarautar Saudiyya su 3, da suke zaune a kasashen turai suka yi batan dabo, kuma dukkansu na sukar lam...
Rating :
5