Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga kungiyoyin da suka hada kawance da su da su goyi bayan kokarin da gwamantin tarayya ke yi akan kawar da cutar siga (diabetes) da sauran cututtkan da ba a iya kamuwa da su ta hanyar shakar isaka a Najeriya.
Ya fadi hakan ne a taron da ma’aikatar kiwon lafiya, gidauniyar ‘World Diabeties’ da kungiyar ‘Strategies for Improving Diabetes Care in Nigeria, SIDAIN’suka shirya mai taken cutar siga da sauran cututtukan da ba a iya kamuwa da su ta hanyar shakar iska; matsaloli da hanyoyin shawo kansu.
Shugaban kula da kiwon lafiyar jama’a na ma’aikatan kiwon lafiya Evelyn Ngige ta wakilci ministan kiwon lafiya Isaac Adewole a taron.
A jawabin da ya bayar Isaac Adewole ya mika godiyarsa na musamman ga kungiyoyin da suka mara musu baya akan kokarin da suke yi wajen kawar da cutar siga sannan ya yi kira ga saurn kungiyoyin da su hada hannu da su domin cimma burinsu.
Ya kara da cewa hakan zai taimaka wa kasan sanin matsayinta game da cututtukan sannan da hanyoyin da za ta bi wajen don kawar da cututtukan.
Isaac Adewole ya ce ma’aikatar kiwon lafiya ta bude sashen kula da mutanen dake fama da cutar sikila (sickle cell anemia) a kowace asibitin gwamnati a fadin kasarnan wanda ya hada da asibitin Ebute Meta a jihar Legas, asibitin gwamnatin dake Keffi jihar Nasarawa, asibitin gwamnatin dake Gombe, asibitin dake Yenagoa jihar Bayelsa, asibitin dake Birnin-Kebbi da asibitin Abakaliki a jihar Ebonyi.
Shugaban kwamitin shirye-shirye na taron Alebiosu C.O yace cututtukan da ba a iya kamuwa da su ta hanyar shakar iska kamar su cutar siga, hawan jini, daji da makamantansu na bada cikas a finnin kiwon lafiya musamman a kasashen da ke ci gaba.
Ya ce cikin mutane miliyan 160 dake Najeriya miliyan 4 na fama da cutar siga inda kashi 70 zuwa 80 bisa 100 na dauke da cutar ba tare da sun sani ba.
Ya ce kamata ya yi a hada karfi da karfe don kawar da cutar kafin lokaci ya kure.
Premium Hausa
Title :
Kashi 70 Zuwa 80 Bisa 100 Na Mutan Dake Dauke Da Cutar Siga A Nigeria Basu Sani Ba
Description : Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga kungiyoyin da suka hada kawance da su da su goyi bayan kokarin da gwamantin tarayya ke yi ...
Rating :
5