Emefiele, ya bayyana cewar yanzu haka akwai yawaitar kasashe da ke kokarin kulla harkallar kasuwanci da Najeriya.
Kasar Saudiyya ce a farko cikin jerin kasashen duniya da ke sayen dabbobi daga kasashen ketare. Kasashen Sudan da Somalia ne ke samar wa Saudiyya mafi yawan dabbobin da take bukata. A shekarar 2016 kasar ta Saudiyya ta bawa kasar Zambiya kwangilar samar da awakai miliyan 1 duk wata.
A duk shekara miliyoyin jama'a ke halartar aikin hajji a kasar Saudiyya, kuma wajibi ne ga duk mai aikin hajji ya sayi tare da yanka dabba a kasar.
source: Naij Hausa
Title :
Kasar Saudiyya na bukatar Dabbobi 120,000 Duk Sati Daga Najeriya
Description : Emefiele, ya bayyana cewar yanzu haka akwai yawaitar kasashe da ke kokarin kulla harkallar kasuwanci da Najeriya. Kasar Saudiyya ce a farko...
Rating :
5