samun maki uku a karawar
Tsohon dan wasan Real Madrid, Jese Rodriguez ne ya ci Arsenal a wasan farko da ya buga wa Stoke City a mako na biyu a gasar Premier a ranar Asabar.
Jese ya koma Stoke ne da murza-leda karkashin koci Mark Hughes daga Paris St-Germain a ranar Laraba.
Dan wasan ya kuma ci Arsenal ne a bugun kwallon da Saido Berahino ya yi masa, bayan da aka koma wasa na biyu bayan hutu da 'yan kwallon suka yi.
Wannan ne karon farko da Stoke ta ci wasa a bana, ita kuwa Arsenal ta ci Leicester City a makon jiya.
Source:BBC Hausa
Title :
Jesse Ya Zura Kwallo Daya Mai Ban Haushi A Ragar Arsenal
Description : samun maki uku a karawar Tsohon dan wasan Real Madrid, Jese Rodriguez ne ya ci Arsenal a wasan farko da ya buga wa Stoke City a mako na biy...
Rating :
5