Kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra IPOB ta ce sam ba ta yarda da janye kiran da kungiyar matasan Arewa suka yi ba cewa yan kabilar Igbon su ci gaba da zama a yankin.
A can baya kungiyar Matasan Arewa AYC sun yi kira ga yan kabilar Igbo da su tattara nasu –inasu su koma yankinsu kafin 1 ga watan Oktoba.
Bayan taro da kungiyar ta yi a Abuja jiya AYC din ta sanar da janye wannan wa’adi da ta bay an Kabilar Igbo din mazauna yankin Arewa.
Amma kuma a wata sanarwa da ta fitar yau, kungiyar IPOB wanda Nnamdi Kanu ke jagoranta ta fitar da wata sanarwa cewa bata amince da wannan janyewa da AYC tayi ba.
IPOB ta ce tana nan a kan bakanta na sai an basu kasar su ta Biafra kuma duk wani dan kabilar Igbo din ya dawo gida kawai kafin 1 ga watan Oktoba din.
Bayan haka sun ce shi kanshi shugaban kasa Muhammadu Buhari ba da gaske yake yi ba, da daga dawowarsa ya sa an kama ‘yan kungiyar matasan arewa din.
Source: Premium Hausa
Title :
IPOB Bata Amince Dan Janye Koran Yan Kabilar Igbo Da Kungiyar Matasan Arewa Tayiba
Description : Kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra IPOB ta ce sam ba ta yarda da janye kiran da kungiyar matasan Arewa suka yi ba cewa yan kabilar Igbon s...
Rating :
5