Hukumar ta sanar da wannan labari ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Talata, a birnin Ikko na jihar Lagos da ke kudancin kasar, inda ta ce motocin da ta kama din kirar jip ne.
Ta kara da cewa, ta kuma kama buhun shinkafa 12,000 da aka shigo da ita daga ta haramtacciyar hanya.
Hukumar ta kuma kama ganyen wiwi sama da buhu 40.
Kudinsu wadannan kayayyaki dai sun kai naira biliyan daya da naira miliyan dari shida.
Ba wannan ne karo na farko da hukumar take irin wannan kamu ba, na kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin kasar.
Source from BBC hausa
Title :
Hukumar kwastam Na Kasa Tayi Wawan Kamu A Legas
Description : Hukumar ta sanar da wannan labari ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Talata, a birnin Ikko na jihar Lagos da ke kudancin kasa...
Rating :
5