Dan majalisar wakilan Najeriya, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya shahara wajen tsayawa ya yi magana a zauren majalisar gaba-gadi ba tare ko da yin dar na yin kuskuren harshen turanci da aka saba magana da shi a majalisar ba.
A Najeriyar dai an dade ana zargin cewa wasu daga cikin 'yan majalisa na shakkar tashi su yi magana a zauren majalisar don gudun kada su yi kure, har a yi musu dariya.
Hon. Gudajin ya shaida wa BBC cewa abinda ya ke ba shi karfin guiwar tashi ya yi magana gaba-gadi a majalisar shi ne ya riga ya sa a ransa cewa duk abinda ya ga na gaskiya ne ya kamata mike ya yi magana, ko kuma in ya ga wata illa, musamman kan abinda ya shafi talaka.
Game da maganganun da ake yi cewa bai iya turanci ba kuwa dan majalisar Hon. Kazaure ya ce ai da ma shi ba bature ba ne bahaushe ne hausa-fulani.
'' Abinda na fahimta shi ne duk lokacin da za ka yi magana a cikin a'umma, duk wata hanya da za ka yi hikima ka isar da sako mutum ya fahimci abinda kake so ya fahimta to ni bukatata ta biya, bana ma tunanin cewa turancina ba daidai bane''
Source: BBC Hausa
Title :
Hon.Gudaji:Nima Kakin Majalisa Ne
Description : Dan majalisar wakilan Najeriya, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya shahara wajen tsayawa ya yi magana a zauren majalisar gaba-gadi ba tare ko d...
Rating :
5