Shugaban kwamitin kula da kiwon lafiyar mahajjata na hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya shawarci mahajjata kan yadda zasu sami kariya ga lafiyarsu a lokacin hajji.
Ga hanyoyin da za a iya bi don samin kariya daga cututtuka:
1. Shafa manshafawa kamar Vaseline ko kuma mankade a matse-matsi domin hana cin jiki saboda yawan tafiya.
2. A rike ruwan sha kowani lokaci.
3. Amfani da lema kowani lokaci.
4. A tabbatar an tsaftace inda ake zama da abinci da ake ci.
5. Saka takalma marasa matsi domin guje wa ciwon kafa.
Bayan haka Ibrahim Kana ya Kara tabbatar wa mahajjatan cewa a shirye suke domin kula da lafiyasu a kasa mai tsarki.
Ya kuma kara da cewa ma’aikatan kiwon lafiya na kusa da mahajjatan dauke da magungun da motocin daukan marasa lafiya a ko’ina a Makka da Madina.
Source: Premium Hausa
Title :
Hanyoyi 5 Da Mahajjaci Zai Kare Lapiyansa Yayin Yin Aikin Hajji
Description : Shugaban kwamitin kula da kiwon lafiyar mahajjata na hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya shawarci mahajjata kan yadda zasu sami kariya ga lafiyar...
Rating :
5