Wani dan majalisar dattawa a Najeriya ya zargi rundunar 'yan sandan kasar da karbar na goro kafin ta yi wa wasu daga cikin jami'anta karin girma.
Sanata Mohammaed Hamma Misau wanda yake wakiltar shiyyar jihar Bauchi ta tsakiya, ya yi zargin cewa: "ana karbar kimanin naira miliyan biyu da rabi a wurin jami'an 'yan sanda da ke bukatar karin girman."
Sai dai zargin da dan majalisar ya yi bai yi wa runduar 'yan sandan kasar dadi ba, domin kuwa sau biyu tana fitar da sanarwa musanta faruwar hakan.
Da farko dai sanatan, ya yi ikirarin cewa a matsayinsa na tsohon jami'in rundunar ya samu korafe-korafe daga manya da kananan jami'an 'yan sanda wadanda suka yi zargin cewa sai mai uwa a gindin murhu ko kuwa wanda aljihunsa ke cike da naira ake yi wa karin girma.
Rundunar 'yan sandan ta ce ta gayyaci sanatan domin ya yi mata karin bayani a kansa, amma ya ki zuwa, kamar yadda kakakin rundunar CSP Jimoh O. Moshood ya shaida wa BBC.
Ya ce, "ba gaskiya ba ne cewa rundunar 'yan sanda na karba cin hanci kafin ta yi wa jami'anta karin girma."
"A lokacin da ya fara yin wannan zargi, sai da babban sufeton 'yan sanda ya kafa kwamiti na musamman domin ya duba batun sannan aka gayyace shi sau biyu domin ya bayar da ba'asi amma ya ki zuwa," in ji rundunar 'yan sandan.
CPS Moshood ya kara da cewa "duk da haka sanatan Misau ya ci gaba da bata wa rundunar 'yan sandan suna saboda cimma wata bukatarsa ta siyasa, shi ya sa a cewarsa ya fito da sabon zargi cewa babban sufeton yan sandan ya wawure naira biliyan 10 na kudin shigar da 'yan sandan suka samu."
Sai dai dan majalisar dattawan ya ce bai kai kansa gaban kwamitin ba ne saboda ba a bi ka'ida ba wajen kafa shi.
Sau da dama dai ana zargin hukumomin gwamnatin Najeriya wurin karbar na goro kafin ko dai su dauki mutum aiki ko kuma su kara masa mukami, zargin da suka sha musantawa.
Source:BBC Hausa
Title :
Hamma Misau Yasa Zare Da Yan Sandan Nigeria
Description : Wani dan majalisar dattawa a Najeriya ya zargi rundunar 'yan sandan kasar da karbar na goro kafin ta yi wa wasu daga cikin jami'anta...
Rating :
5