A yau ne, Manyan hafsoshin sojin Najeriya suka isa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na yakar kungiyar Boko Haram kwanaki biyar bayan da Mukaddashin Shugaban kasa ya ba su umarni.
A makon da ya gabata ne Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarce su da su koma can bayan wani mummunan hari da kungiyar ta kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 40.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya Janar Usman Kuka-Sheka ya ce da sanyin safiyar ranar Talata ne hafsoshin son suka isa birnin, wanda shi ne cibiyar masu tayar da kayar bayan.
Ya ce babban Hafsan Hafsoshin kasar Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ne ya jagoranci sauran hafsoshin sojin da suka hada da shugaban sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai da na sama Air Marshal Sadique Abubakar. Janar Kuka-Sheka ya ce babban hafsan rundunar sojin ruwa na kasar ne kawai ba ya cikin tawagar saboda ya yi tafiya, amma shi ma wakilansa na can.
Title :
Hafsoshin Soja Sun Isa Maiduguri Kwanaki Biyar Bayan Ba Su Umarnin Yin Hakan
Description : A yau ne, Manyan hafsoshin sojin Najeriya suka isa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na ...
Rating :
5