Tottenham na daf da sayen dan wasan Ajax mai shekara 21, Davinson Sanchez,in ji Telegraph.
Manchester City ta shirya domin ta bai wa West Brom fam miliyan 22 don sayen keftin dinta dan shekara 29 Jonny Evans, bayan an yi watsi da tayin fam miliyan 18 da ta yi. Kazalika City ta shirya domin ta kusan rubanya albashin dan wasan Arewacin Ireland na fam 75,000 a ko wane mako, in ji Mirror
An yi watsi da tayin da Chelsea ta yi na fam miliyan 63 ga dan wasan Jueventus mai shekara 26 Alex Sandro, in ji Mirror
Daraktan wasannin Barcelona, Robert Fernandez, ya ce zai yi wuya a iya sayen dan wasan tsakiyar Liverpool mai shekara 25, Philippe Coutinho, domin babu damar sallama a yarjejeniyarsa, in ji Liverpool Echo
Barca za ta ci gaba da gwagwarmaya wajen sayen dan wasan Brazil Coutinho, har sai lokacin da aka rufe kasuwar 'yan wasa yayin da ake ci gaba da tsammanin Barcelona za ta sake taya dan wasan, in ji Telegraph
Dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, mai shekara 28, ya ce ba zai sake komawa Stamford Bridge ba, kuma yana son ya sake komawa Atletico Madrid, in ji Telegraph
Everton za ta iya yunkurin daukar aron dan wasan Spaniya Costa daga zakarun Firimiya, in ji Sun.
Dan wasan bayan Spurs Kevin Wimmer, mai shekara 24, yana tattaunawa da West Brom kan yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 15, in ji Telegraph
Ita ma Stoke tana shaukin sayen dan wasan Austria Wimmer, in ji Stoke Sentinel
Dan wasan bayan Arsenal da Brazil Gabriel, mai shekara 26, yana dab da komawa Valencia a wata yarjejeniyar kudi fam miliyan 10, in ji Evenin Standard
Manchester United ba ta yanke kauna ba kan sayen dan wasan gefe Ivan Perisic, mai shekara 28, duk da cewar fam miliyan 39 ne tayin da suka yi wa Inter Milan, in ji Mirror
Source: BBC Hausa