KASUWAR SAYAYYAR YAN WASA- JUMA'A 4/8/2017
1. Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya amince cewa dole sai kulob ya sayar Gareth Bale mai shekaru 28 kafin ya samu damar sayan dan gaban Monaco Kylian Mbappe mai shekaru 18.
2. Manchester United na bibiyar abubuwan dake faruwa a Real Madrid kuma za ta kai tayin £90m ga dan Wales din Bale.
3. Kocin Red Devils Jose Mourinho ya gamsu cewa zai iya sayan Bale a kasa da £90m.
4. Dan gaban Chelsea Diego Costa zai mika takardar neman barin zakarun Premier din.
5. Zakarun Faransa Monaco na shirin kai tayin £45m don sayan dan gaban Arsenal Alexis Sanchez mai shekaru 28.
6. Tottenham na sha'awar sayan dan gaban Genoa Giovanni Semione mai shekaru 22, wanda da ne ga kocin Atletico Madrid Diego.
7. Chelsea na shirin yin takara da Liverpool akan Van Dijk, inda za ta mikawa Southampton tayin £50m ga dan bayanbkasar Holland din.
8. Barcelona ta tuntu6i Monaco akan ko za ta sayar mata da dan gaba Kylian Mbappe mai shekaru 22.
9. Barcelona za ta yi amfani da kudin da ta sayar da Neymar wajen neman dan gaban Chelsea Eden Hazard mai shekaru 26, da dan gabam Liverpool Philippe Coutinho mai shekaru 25.
10. Barca ba za ta yi yinkurin sayan dan gaban Atletico Madrid Antoine Griezmann mai shekaru 26 ba, bisa tafiyar Neymar.
11. Kulob din na Sifaniya ka iya maye gurbin Neymar da dan gaban Borussia Dortmund dan kasar Faransa Ousmane Dembele mai shekaru 20.
12. Dortmund ta yi watsi da tayin Arsenal akan Dembele.
13. Chelsea za ta duba yiwuwar sayan dan tsakiyar Leicester Danny Drinkwater mai shekaru 27 a maimakon dan wasan Bayern Munich Renato Sanches mai shekaru 19.
14. Kocin Arsenal Arsene Wenger ya fadawa dan gaba Alexis Sanchez cewa ba za a sayar dashi ga wata kungiya da take a Ingila ba.
15. Manchester United na sha'awar sayan dan wasan bayan PSG Serge Aurier mai shekaru 24, wanda a yanzu haka an dakatar dashi daga shiga kasar Birtaniya.
16. Liverpool bata da sha'awar yan wasan tsakiyar Barcelona Andre Gomes da Rafinha, wadanda ake ambata cikin wanda za a iya yin musaya dasu a cinikin Coutinho.
17. Dan gaban Brazil Neymar ya ce "abin bakin ciki ne" da mutane ke cewa cinikin da ba a ta6a yin kamarsa a duniya na £200m (€222m) na barinsa Barcelona zuwa PSG saboda kudi ne, inda ya ce abin ba haka bane. Dan shekaru 25 din zai rika kar6ar albashin £40.3 duk shekara. PSG za ta kashe kusan £400m akan Neymar bisa yarjejeniyar kwantaragin da ya sanya hannu.
Title :
Hada-Hadan 'yan Wasa
Description : KASUWAR SAYAYYAR YAN WASA- JUMA'A 4/8/2017 1. Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya amince cewa dole sai kulob ya sayar Gareth Bale mai ...
Rating :
5