Gwamnonin jihohin Kudu maso gabacin kasar nan, na can na ganawar sirri da dan taratsi Nnamdi Kanu. Taron wanda gwamnoni biyar ke halarta, ya na gudana ne Gidan Gwamnatin Jihar Enugu.
Sakataren yada labaran Gwamnan Jihar Enugu, David Umani, ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook a yau Laraba.
A bayanin da ya aika a shafin nasa, Uzor ya ce ana sa ran kurarin da mabiya Nnamdi Kanu su ka yi na cewa ba za a yi zabe a jihar Anabra ranar 18 Ga Nuwamba ba, zai kasance shi ne babban ajandar taron.
Wannan ne karo na farko da Kanu ke ganawa da gwamnonin, bayan ya sha kin amsa kiran da su ka sha yi masa na su zauna a nemi maslaha.
Source: Premium Hausa
Title :
Gwamnonin Kudu Maso Gabas Na Ganawa Da Nnamdi Kanu
Description : Gwamnonin jihohin Kudu maso gabacin kasar nan, na can na ganawar sirri da dan taratsi Nnamdi Kanu. Taron wanda gwamnoni biyar ke halarta, ya...
Rating :
5