Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Lagas ta ba da sautun buhuhunan shinkafa har tireloli guda 70 saboda siyar wa al’ummar jihar ta kan farashi mai rahusa domin bikin babban Sallah.
Za’a fara siyar da shinkafar ne a yau Alhamis, 24 ga watan Agusta har zuwa bayan bikin babban Sallah.
A bisa rahoto, za’a bayar da buhu mai girman 50kg a kan farashin naira 12,000, yayinda za’a siyar da karamin buhu mai cin 25kg kan naira 6,000 sannan 10kg zai zo a kan naira 2,500.
A cewar Toyin gwamnatin tayi haka ne saboda tallafa wa musulmai a yayin bikin Sallah babba wanda ke hanya.
Source: Naij Hausa
Title :
Gwamnatin Jihar Legas Ta yi Odan Tireloli 70 Na Buhuhunan Shinkafa
Description : Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Lagas ta ba da sautun buhuhunan shinkafa har tireloli guda 70 saboda siyar wa al’ummar jihar ta kan ...
Rating :
5