Gwamnatin jahar Sokoto ta bada tallafi ga Mal Lawwali mai shinkafa Illela, wanda matar shi ta haifi yan hudu a satin da ya gabata.
Kwamishinan maaikatar jin dadin jama'a Alh Sirajo Gatawa ne ya gabatar da kayan ga iyalan yan hudun a gidansu da ke cikin garin Illela, a lokacin gabatar da kayan Kwamishinan Yace Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya umurce Shi da ya gabatar da wannan tallafin biyo bayan sanar da Shi da aka yi game da haihuwar.
Yace Gwamnan na iya kokrin shi wurin kula da jin dadin alumma saboda duk lokacin da aka nemi ya bada tallafi ga wanda ke bukata yana badawa, ya bayyana sakon Gwamna na taya murnar samun wannan baiwar da Allahu ya yi musu tare da addua samun lafiya ga uwar da abin ciyar wa ga uban.
Gatawa ya mika tallafin kayan abinci da tufafin yara da na mahaifiyarsu da gadajen jarirai da katihu masu gidan sauro, da madararar jarirai da sauransu ga iyalan yaran mata yan hudu.
Haka ma ya mika ma mahaifin yaran kudi naira duba dari biyar daga Gwamna Tambuwal. Shugaban karamar hukumar Illela ya godewa gwaman kan tallafin da aka bada,kuma ya hada matar da jamian kiyyon lafiya don bada shawarwarin kan yadda zaa kula da su .
Mal Lauwali da matar shi Shafaatu sun nuna farincikinsu da godiya ga Gwamana Tambuwal kan daukin da aka kai musu tare da rokon Allah ya biya shi
Title :
Gwamnan Jihar Sokoto Ya Bada Tallafi Wa Mal Lawali Da Matarsa
Description : Gwamnatin jahar Sokoto ta bada tallafi ga Mal Lawwali mai shinkafa Illela, wanda matar shi ta haifi yan hudu a satin da ya gabata. Kwamish...
Rating :
5