Mahaukaciyar Guguwa mai karfin gaske, ta afkawa jihar Texas da ke Amurka, wadda masana suka bayyana ta a matsayin babbar masifa ga jihar da ma makwabtanta.
Guguwar mai tafiyar kilomita 195 a sa’a guda, da masana suka yi wa lakabi da Huriccane Harvey, ana sa ran ta zama mafi karfin wadda ta taba afkawa Amurka tun bayan makamancin hakan a shekarar 2005.
Tun kafin guguwar ta isa jihar, shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan takardar ayyana Texas a matsayin jihar da ke fuskantar masifa, tare da bada umarnin fitar da kudaden kai agaji.
Allah ya kiyaye
Title :
Guguwa Mai Hatsari Ta Afkawa Wa Texas
Description : Mahaukaciyar Guguwa mai karfin gaske, ta afkawa jihar Texas da ke Amurka, wadda masana suka bayyana ta a matsayin babbar masifa ga jihar da...
Rating :
5