Gobara ta tashi a wani otal a Makka, wadda ta yi saurin jan hankalin mahajjata da kuma jamai’an tsaro a safiyar Litinin.
Otal din wanda ke tsakiyar birnin Makka, an bayyana cewa jamai’an tsaro sun tserar da dukkanin wadanda ke cikin sa.
A wannan aikin Hajji na 2017, an kiyasta sama da mutane miliyan biyu ne za su yi aikin Hajji, daga kasashe daban-daban na duniya.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN, ya ruwaito takwaran sa na Xinhua da ke kasar Chana cewa jami’in tsaron cikin gida na Makka mai suna Nayef al-Sharif, ya ce ba a samu wanda ya ji rauni ba, inda ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sanadiyyar wata na’urar sanyaya daki da ta samu matsala. Wutar ta tashi ne a hawa na 8 na otal din da ke gundumar Aziziyah cikin Makka.
Sherif ya kara da cewa dukkan baki mahajjata 800 da ke cikin otal din akasarin su ‘yan kasar Turkiyya da Yemen ne kuma tuni har sun koma cikin otal din sun don ci gaba da gudanar da sha’anin su.
Source: Premium Hausa
Title :
Gobara Ya Tashi A Wani Otal A Saudiyya
Description : Gobara ta tashi a wani otal a Makka, wadda ta yi saurin jan hankalin mahajjata da kuma jamai’an tsaro a safiyar Litinin. Otal din wanda ke ...
Rating :
5