A Nigeria, ga alamu kokarin da hukumomin kasar ke yi na fadada yaki da cin hanci da rashawa zuwa matakin kasa ya fara tasiri wajen kama wadanda ake tuhuma da almundahana.
Misali a jihar Kaduna kadai, hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta EFCC ta ce ta kama mutane fiye da 860 da ake tuhuma da hannu a almundahana cikin 'yan watanni da bude ofishinta a can.
A cikin wata sanarwa, Shugaban Hukumar a shiyyar Kaduna, Ibrahim Baffa, ya ce an kakkama mutanen ne sakamakon koke-koke har 220 da aka shigar gaban hukumar tasa kan wadannan mutanen.
Allah ya Kyauta
Source: BBC hausa
Title :
EFCC Ta Rafke Mutane 865 A kaduna
Description : A Nigeria, ga alamu kokarin da hukumomin kasar ke yi na fadada yaki da cin hanci da rashawa zuwa matakin kasa ya fara tasiri wajen kama wada...
Rating :
5