Dattawan Manchester United za su karbi bakuncin na Barcelona a wasan sada zumunta domin tuna wadan da suka mutu a harin ta'addacin da aka kai biranensu.
Tsoffin 'yan wasan da za su buga wa United karawar sun hada da Edwin van der Sar da Ruud van Nistelrooy da Ji-sung Park da kuma Wes Brown.
Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Old Trafford da Edgar Davids da Patrick Kluivert da Gaizka Mendieta da kuma Eric Abidal.
Dattawan za su daura bakin kyalle a hannunsu da kuma sunan biranensu a bayan rigunan da kowa zai saka a fafatawar da za su yi a ranar Asabar a Old Trafford.
A cikin watan Mayu ne aka kai harin ta'addanci a birnin Manchester daga baya aka kai hari a birnin Barcelona da na Cambrils a farkon watan nan.
Source: BBC Hausa
Title :
Dattawan United Zasu Gwabza Dana Barcelona
Description : Dattawan Manchester United za su karbi bakuncin na Barcelona a wasan sada zumunta domin tuna wadan da suka mutu a harin ta'addacin da ak...
Rating :
5