DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH
Kwanaki goman farko na watan Zul Hijjah kwanaki ne masu darajar gaske, kwanaki ne da ya kamata musulmi su yawaita ayyukan ibada a cikinsu: Azumi, da Salloli, da Kabbarori, da ba wa mabukata sadaka, da sauransu.
Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 969 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Babu wasu ranaku da aikin alheri ya fi soyuwa cikinsu a wurin Allah kamar kwanaki goman farko na watan Zul Hijjah. Sai Sahabbai suka ce wa Manzon Allah: Koda yin jihadi ne cikin tafarkin Allah? Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: Na'am, koda yin jihadi ne cikin tafarkin Allah, amma banda mutumin da ya fita jihadi da kansa da kuma dukiyarsa, sannan bai dawo da kome ba daga cikin abin da ya fita da shi)). Intaha.
Imamul Bukharii ya ce cikin Sahihinsa, a babin falalar aiki cikin kwanakin Tashriq: ((Ibnu Umar, da Abu Hurairah sun kasance suna fita zuwa kasuwa cikin kwanakin nan goma suna yin kabbara, sannan mutane na yin kabbara saboda kabbarorinsu)). Intaha.
Alhafiz Ibnu Hajar ya ce cikin Fathul Barii 2/534: ((Abin da ke bayyana shi ne: Su kwanaki goman farko na Zul Hijjah sun samo darajarsu ne ta hanyar kasancewarsu wani irin wuri da manyan ibadodi ke haduwa a cikinsa, wadannan kuwa su ne: Salla, da Azumi, da Sadaka, da Hajji, wannan abin ba ya faruwa cikin wasun wadannan kwanakin)). Intaha.
Idan wani ya ce: Ai Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 2439 da isnadi sahihi daga Nana A'isha Allah Ya Kara mata yarda ta ce: ((Ban taba ganin Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi azumi koda sau daya ba a cikin kwanaki goman farko (na Zul Hijjah) ba)). Intaha.
Sai a ce da shi: Maluma sun ce wannan hadithi yana nuni ne a kan irin yadda wani lokaci Annabi mai tsira da amincin Allah yake barin wani aikin lada saboda tsoron kada a farlanta shi a kan al'ummarsa, ba wai yana hana yin azumi ba ne cikin wadannan kwanaki.
BABU ASKI DA YANKAN FARSHE DA DEBE WANI ABU DAGA JIKI
Da zarar an ce watan Zul Hijjah ya kama to dukkan mai niyyar yin layya kada ya debe wani abu daga fatar jikinsa: kada ya aske wani abu na gashin jikinsa ko gashin kansa, kada ya yanke wani abu na farshensa.
Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 1977 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Idan kwanaki goman farko na watan Zul Hijjah suka shigo, sannan dayanku ya yi niyyar yin layya to, kada ya taba wani abu na gashinsa, da fatar jikinsa)). A wata riwaya kuma ya ce: ((Ya kame kansa daga gashinsa da farshensa)). Intaha.
Amma wasu Maluma sun ce: yin aski ko yanke farshe ga mai niyyar yin layya cikin wadannan kwanaki haramun ne, wasu kuwa suka ce makruhi ne kawai bai kai haramci ba, wasu kuwa suka ce halal ne a yi hakan.
To, amma abin da muke gaya wa yan'uwa Musulmi a nan shi ne: Abin da sunnar Annabi take nunawa shi ne yin hakan haramun ne, saboda asalin lamarin Shari'ah shi ne: duk abin da Annabi ya hana yin shi to yin nasa haramun ne, sai in an sami wani dalili daban da zai iya fidda shi daga wannan asalin, a wannan mas'alar kuwa babu wannan dalilin.
Muna rokon Allah ya taimake mu, Ya ba mu ikon ayyukan alheri cikin wadannan kwanakin.
Title :
DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH
Description : DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH Kwanaki goman farko na watan Zul Hijjah kwanaki ne masu darajar gaske, kwanaki ne da ya kam...
Rating :
5