Shugaban Gidauniyar Dangote, Aliko Dangote, ya ware naira bilyan 200 da zai kashe wajen gina jami’ar da duniya za ta yi tutiya da ita a Abuja.
Tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Julius Okojie, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gina jami’ar, ya shaida cewa za a gina makarantar ne da nufin amfani da ilmin fasaha wajen bincike da inganta tattalin arziki.
Okojie, wanda ya jagoranci tawagar sa su ka kai ziyara ga Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i, Farfesa Abubakar A. Rasheed, ya shaida masa cewa jami’ar fasaha ce ake da kudirin ginawa, inda ya nemi goyon bayan hukumar wajen ganin an tabbatar da gina jami’ar.
Tawagar wadda ta kunshi shugabar Gidauniyar Dangote, Hajiya Zouera Yousouffou, ta bayyana cewa Dangote dama ya na da burin ganin ya gina kasaitacciyar jami’ar nazari da binciken fasaha wadda za a samar wa ingantattun kayan aiki da mashahuran malaman da ake tinkaho da su a duniya.
Da ya ke masu jawabin maraba, Farfesa Rasheed ya jinjina wa Dangote kan wannan gaban-gabarar aiki da ya kinkimo. Ya na mai cewa dama ai wasu kaya sai amale, ya kuma sha alwashin cewa hukumar sa a shirye ta ke ta bayar da duk irin goyon bayan da ake bukata domin ganin wannan kasaitaccen aikin alheri ya tabbata.
Sai dai kuma ya kara da ba su shawarar kada su tsaya a kan fannin fasaha kadai, ya na mai cewa kamata ya yi wannan jami’a ta kunshi sauran fannoni daban-daban, ba wai a takaita ta kan fannin fasaha kadai ba.
Daga nan ya kara bayar da shawarar cewa kamata ya yi kwamitin aikin gina maarantar su kara fadada bincike da tuntubar wasu jami’o’in ciki da wajen kasar nan, domin su samu nasarar kafa jami’ar da za ta bambanta wajen inganci fiye da wadanda ake da su.
Da ta ke jawabi, Yousouffou ta ce gidauniyar tuni ta rigaya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 200 da za a kashe wajen gina makarantar.
Ta kara da cewa tuni an ma rigaya an sayi makeken filin da za a gina katafariyar hedikwatar jami’ar a Abuja.
Source: Premium Hausa
Title :
Dangote Zaikashe Naira Biliyan 200 Wurin Gina Jami'a A Abuja
Description : Shugaban Gidauniyar Dangote, Aliko Dangote, ya ware naira bilyan 200 da zai kashe wajen gina jami’ar da duniya za ta yi tutiya da ita a Abuj...
Rating :
5