Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi.
Hafsa, wacce ake kira 'Barauniya' ko 'Yar Fim a Kannywood, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza.
Ta kara da cewa, "Yin fim ya fi aikin gwamnati domin kuwa abin da nake samu ma'aikacin gwamnati ba zai samu ba."
Da fim nake yin hidimomina da na iyayena da na 'yan uwana," in ji jarumar.
Ta kara da cewa ta koyi darasi da dama daga fim din "Barauniya" wanda shi ne na farko da ta fara yi a Kannywood.
Na fahimci "yadda barayi ke sata da kuma yadda satar ke tagayyara wadanda aka yi wa".
"Na nuna jarumta da rashin tausayi da dabaru irin na barayi," a cewar Hafsat.
"A zahiri ni ba barauniya ba ce, ba ni da son zuciya amma da yake so ake a nuna yadda ake yin sata da kuma irin illarta ga al'umma shi ya sa na amince na taka wannan rawa," in ji ta.
Jarumar, wadda ta soma fim a watan Disambar 2016, dalilin yin fim din Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.
Ta ce kowanne wata tana yin fim uku zuwa hudu saboda "amincewar da furodusoshi" suka yi mata wajen taka rawa a manyan fina-finai.
Jarumar ta ce tana ci gaba da "gogewa shi ya sa ma na fito a fina-finai irin su 'Yar Fim da Rariya da Maimunatu da Wata Ruga da sauransu."
Sai dai masu sharhi na ganin akwai jan aiki a gabanta ganin yadda Kannywood ke cike da jarumai masu tashe.
Source: BBC Hausa
Title :
Dalilin Dayasa Na Fito A Barauniya-Hafsat Idris
Description : Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka...
Rating :
5