A wannan ‘yar gejeriyar tattaunawa da aka yi da shahararriyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi, jarumar ta tabo batun halin da masana’antar fim take ciki, har ila yau ta dan yi albishir ga masoyanta kan sabon shirinta.
Kwana biyu an ji ki shiru a finafinai, ko akwai wani abu a kasa ne?
To, gaskiya ba zan ce an ji shiru ba, kawai da hutu ne kamar yadda kowa yake yi. Kuma na yi hakan ne domin na mayar da hankali kan sabon fim dina da yanzu haka muke shiryawa, yana nan fitowa nan ba da jimawa ba.
Duk inda jarumi ko mai shirya fim yake, akwai bukatar ya rika nutsuwa domin yin nazarin abu mai kyau. Fim ba don tsirarun mutane ake yi ba, ana yi ne saboda al’umma da yawa. Saboda haka, dole ana bukatar yin tunanin na kwarai ta yadda za a zo wa da mutane abun da za su yi saurin karba.
Finafinai nawa ne aka sa kike yi yanzu?
Ina da finafinai da yawa wadanda aka kawo min labarinsu. Ba lallai in ce Eh ko A’a ba, tun da komai yana tafiya ne bisa tsari. Ba komai ne zan bayyana ba dalla-dalla a halin da ake ciki yanzu ba. Albishin din da zan yi wa masu kallon finafinai Hausa shi ne, sabon shirin da muke kokarin zuwa da shi, hakika zai kayatat matuka da gaske.
Na yi maganar finafinai da yawa, amma ba kowane ne aka cimma matsaya ba. Zamowa wadda mutane ke so ba yana nufin kowane fim sai na fito a ciki. Hutun da na tafi yana da alaka da sabon tunanin da nake son zuwa da shi a wannan masana’anta. Shi fim, kamar yadda aka sani, hanya ce ta isar da sako ta hanyar nishadi, saboda haka lallai ka zo da sakon da zai burge mutane.
Ko za ki iya shaidawa mutane sunan fim din?
To, yanzu dai mun rada masa suna KARMA.
Shin kun kusan kammala shi wannan shirin ne?
Zuwa yanzu zan iya cewa mun kammala kusan kaso 70 cikin 100. Amma ka san yanzu abubuwa sun canja, saboda haka muna da sabbin hanyoyi da muka bullo da su na tallata wannan fim da zai dace da yadda ake yi a fadin duniya. Mun ajiye tunanin kasuwanci fim da gama-gari. Wannan karo sabbin tsare-tsare ne da muke sa ran haska fim din a wasu kasashe, ba wai Nijeriya kawai ba.
Yaushe za a saki fim din?
Ba zan fadi wannan ba a halin yanzu ba. Abin da na sani shi ne muna aiki tukuru don tabbatar da ganin mun kayatar da mutane. Lokaci ne kawai zai bada damar haka. Idan lokaci ya yi kowa zai ji labari.
Ko za ki dan yi tsokaci game da abin da fim din ya kunsa?
Ba yanzu ba tukun. Ina da dalilaina ba boye wasu abubuwan da suka shafi lamari irin wannan kafin a kammala. A wasu lokutan, idan ka bayyana abu, a karon farko sai ka ga ka ragewa mutane karsashi. Amma ina tabbatarwa da masu kallon finafinan Hausa cewar, Nafisa Abdullahi da aka saba gani, to a cikin wannan shiri ta canja, domin za ta bayyana ne a wata siffa daban. Shi ya sa nake ta fadi tunanin da muka yi ya ba mu damar kirkiro abubuwa da yawa. Duk lokacin da ka samu nutsuwar yin tunani, to babu shakka za a zo da abu mai kayatarwa.
Fim dina da zai fito nan gaba, rawar da na taka mutane ba su taba gani na a cikinta ba. Ni ce dai, amma masu kallo za su ce, tabbas mun ga sabon abu
Title :
Dalilin Dayasa Na Boye Wasu Abubuwan Dasuka Shafeni-Nafisat Abdullahi
Description : A wannan ‘yar gejeriyar tattaunawa da aka yi da shahararriyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi, jarumar ta tabo batun halin da masana’anta...
Rating :
5