A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan wata cutar da ba a san hakikaninta ba ta barke.
Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar jihar ta fitar ta ce wadanda suka kamu da cutar suna cin ciwon mara baya ga amai da gudawa da suke yi.
Sanarwar ta ce daga farko dai an kai wadanda suka kamu da cutar asibitin koyarwar gwamnatin tarayyar kasar da ke jihar Edo, inda aka gane cewar ba zazzabin Lassa ba ne ke damunsu.
Rahotanni sun ce cutar ta fi shafar al'ummomin Fulani da ke jihar ne, wadanda yawancinsu makiyaya ne.
Tawagar lafiya ta jihar ta je yankunan da annobar ta barke, inda suka yi bincike kan ruwan sha da hanyoyin samun abincin mutanen wajen.
Source: BBC Hausa
Title :
Cutar Da Baa Saniba Ya Kashe Mutane Dayawa A Nigeria
Description : A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan wata cutar da ba a san hakikaninta ba ta barke. Wata sanarwa...
Rating :
5