Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta doke Tottenham da ci 2-1 a wasanta na biyu a gasar Premier bana.
Tottenham tana gida ne, amma an yi wasan ne a filin Wembley saboda ana aikin gyaran filin wasan kungiyar wato White Hart Lane.
Chelsea ce ta fara zura kwallo a ragar Tottenham, minti 24 da fara wasa ta hannun Marcos Alonso.
Wasan ya koma 1-1 ne a minti na 82, lokacin dan wasan Chelsea, Batshuayi, ya yi kuskuren jefa kwallo a ragarsu.
Ana saura minti biyu a tashi wasa ne Alonso ya kara daga ragar Tottenham.
Wannan ne wasa na farko da Chelsea ta samu nasara a gasar Premier bana, bayan da ta yi rashin nasara a wasanta da Burnley makon jiya.
Source: BBC Hausa
Title :
Chelsea Ta Doke Tottenham Ci 2 Da 1
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta doke Tottenham da ci 2-1 a wasanta na biyu a gasar Premier bana. Tottenham tana gida ne, amma an yi was...
Rating :
5