Shahararren mai bada Nishadi, Charles Oputa(Charly Boy), bai kula da maganar 'yan sanda da suka yi na cewar ya zube kasa a wata zanga-zanga a Abuja don jawo hankalin mutane
Ya shaida wa Sunday Scoop cewa, "Gaskiya ne na fadi. Barkonon tsohuwa ya sa ni jiri kuma na fadi. Na kuma tsaya da maganata cewa wani dan sanda ya buge ni da bindiga. Gwamnatin karya ce kuma haka 'yan sandan ma. Kowa yana cikin hanyar yaudara. Idan mutanen Najeriya sun yarda da gwamnati da 'yan sanda, to, shikenan. Na gaya muku abin da ya faru. Ba aiki na ba ne don yin bayani game da ko mai ya faru. Ina mayar da hankali ga abin da muke yi. Kuskuren da 'yan sanda suka yi shine su fuskanci masu zanga-zangar kamar su (' yan sanda) sun zo domin yaki.
Source: Naij Hausa
Title :
Bazamu Daina Zanga Zanga Ba Har Sai Ya Dawo - Charlie Boy
Description : Shahararren mai bada Nishadi, Charles Oputa(Charly Boy), bai kula da maganar 'yan sanda da suka yi na cewar ya zube kasa a wata zanga-za...
Rating :
5