Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya aike wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar, inda yake sanar da ita cewa zai koma bakin aikinsa, bayan dawowarsa daga hutun jinya da ya yi a Birtaniya.
Shugaba Buhari ya koma Najeriya ne ranar Asabar 19 ga watan Agusta, kuma a wasikar da ya rubuta wa majalisar dattijai da ta wakilan kasar, ya shaida musu cewa zai koma bakin aikin nasa ne a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce, Shugaba Buharin ya yi hakan ne kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
A cikin wasikar, shugaban ya rubuta cewa, "Kamar yadda sashe na 145 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada, Na rubuta wannan wasika ce domin na sanar da ku cewa na koma bakin aikina a matsayin shugaban Najeriya, daga ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2017, bayan na dawo daga ganin likitocina a Birtaniya."
A ranar 7 ga watan Mayun 2017 ne, Shugaban Buhari ya mika ragamar gwamnati ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban kasa, a lokacin da ba ya nan.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Turawa Majalisa Da Wasika
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya aike wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar, inda yake sanar da ita cewa zai koma bakin aikinsa, baya...
Rating :
5