Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah.
Hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta sun nuna manyan jami'an gwamnati da Sarakuna suna tarbar shugaban kasar.
Cikin wadanda suka tarbe shi har da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sarakunan Katsina da Daura.
A ranar 19 ga watan nan ne Shugaba Buhari ya koma Najeriya, bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a birnin London.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Tafi Bikin Sallah Daura
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah. Hotuna...
Rating :
5