Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin gina hanyoyin jiragen kasa daga Kano zuwa Daura da kuma Kano zuwa Maiduguri.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana haka, inda ya ke cewa matakin wani yunkuri ne na Gwamnatin kasar wajen ganin an shawo kan matsalolin sufuri da suka addabi 'yan Najeriya.
Ministan ya kuma ce Buhari ya amince da gina layin dogo daga Port Harcourt zuwa Maiduguri da Makurdi zuwa Jos da Gombe zuwa Yobe zuwa Maiduguri sai kuma Jigawa zuwa Jamhuriyar Nijar.
Source: Rfi Hausa
Title :
Buhari Ya Amince Da Gina Sabbin Layin Dogo
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin gina hanyoyin jiragen kasa daga Kano zuwa Daura da kuma Kano zuwa Maiduguri. Minista...
Rating :
5