Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin kan yadda tattalin arzikin kasar ya fara gyaruwa ne, wasu 'yan kasar suka fara yi masa raddi musamman a kafofin sada zumunta.
Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.
Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa'o'i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana
Sai dai masu muhawara a shafinmu na Facebook sun bayyana mabambantan ra'ayoyi kan hakan.
Ga kadan daga cikinsu:
Haruna Suleiman Utono ya ce, "Har yanzu talakan Najeriya bai san da farfadowar tattalin arziki ba. Saboda har yanzu babu abin da ya sauya".
"To a ina arzikin yake farfadowa bayan kun jefa kasa cikin talauci da yunwa", in jiUsman Ibrahim
Shi kuwa Abubakar Kawu Girgir yabawa ya yi da kalaman shugaban kasar yana mai cewa "Hakika muna godiya da irin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na ganin ya dawo mana da tattalim arzikinmu".
Shi ma Abdurahaman Gangarawa cewa ya yi, "Allah Ya sa alheri kan farfadowar tattalin arzikin Najeriya, ya ninninka farfadowarsa, ya ba mu ikon amfana da shi."
Source:BBC Hausa
Title :
Buhari Ne Ya Jefa Nigeria A Yunwa Da Talauci
Description : Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin kan yadda tattalin arzikin kasar ya fara gyaruwa ne, wasu 'yan kasar...
Rating :
5