Rahotanni dake fitowa daga fitowa daga garin Madagali na jihar Adamawa yace an sami hare-haren Boko Haram a daren jiya duk da cewa an ci galabar mayakan an kore su a baya.
Babu dai labarin ko an rasa rayuka a harin, amma an san Boko Haram da sata, barnatar da dukiya dama dibar 'yan mata domin bautarwa.
Kauyukan dai da abin ya shafa sun hada da Nyibango da Muduvu karkashin karamar hukumar Madagali, kuma Chiyaman na karamar hukumar Yusuf Muhammed ya tabbatar da hakan.
Allah ya sauwake
Source: Naij Hausa
Title :
Boko Haram Takai Sabon Hari Wasu Garuruwa Biyu A Adamawa
Description : Rahotanni dake fitowa daga fitowa daga garin Madagali na jihar Adamawa yace an sami hare-haren Boko Haram a daren jiya duk da cewa an ci gal...
Rating :
5