Fadar shugaban Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasar yake aiki daga gida bayan ya dawo daga jinyar sama da kwana 100 da ya yi a Landan.
Kakakin shugaban Malam Garba Shehu, ya bayyana wa BBC cewa shugaba Buhari ya ci gaba da aiki a gida ne domin kwari da beraye sun lalata abubuwa a ofishinsa.
Inda ya kara da cewar akwai ofisoshi biyu a fadar shugaban, daya a hade da gida, daya kuma daga waje.
Malam Garba ya ce ofishin da yake daga waje ne kwarin suka yi barna, kuma ba a tashi gane barnar ba sai lokacin da aka ji shugaban kasar zai dawo kasan
Fadar shugaban kasar ta ce yanzu haka kamfanin Julius Berger na nan yana aikin gyaran ofishin.
Da aka tambaye shi ko rashin lafiyar ce ta sa shugaban ya ci gaba da aiki daga gida, sai kakakin ya ce "ai duk wanda ya ga Shugaba Muhammadu Buhari, ba zai yi wannan maganar ba. Amman ita siyasa ta Najeriya haka ta gada."
Ya ce shugaban yanzu zai fara aiki ne da tattaunawa da shugabannin sassa daban-daban na gwanatin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Beraye Da Kwari Sun Hana Buhari Shiga Ofishinsa
Description : Fadar shugaban Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasar yake aiki daga gida bayan ya dawo daga jinyar sama da kwana 100 da ya yi ...
Rating :
5