Wata coci mai suna Believers World Ministry, Fire Arena dake da sansani a karamar hukumar Kuje a garin Abuja tayi mabiyanta sha-tara-ta-arziki inda ta raba masu magunguna tare da kiran likitoci su duba su a kyauta, rarraba kayayyakin sawa da litatafan karatu duk a kyauta.
Cocin dai ta shirya wannnan kwarya-kwaryan abun arzikin ne dai a ranar Lahadin da ta wuce kwana daya kenan da dawowar shugaba Muhammadu Buhari Najeriya bayan shafe kwanaki sama da 100 yana jinya a kasar Ingila.
Yace cocin ta bullo da wannan shirin ne domin ta taimakawa mabiyanta masu kananan karfi domin suma su samu saukin rayuwa su su kuma ji dadin ci gaba da zama a matsayin su na mabiyan nasu.
Source: Naij Hausa
Title :
Bayan Dawowan Buhari,Wata Coci Tayi Wa Mabiyanta Shatara Na Arziki
Description : Wata coci mai suna Believers World Ministry, Fire Arena dake da sansani a karamar hukumar Kuje a garin Abuja tayi mabiyanta sha-tara-ta-arzi...
Rating :
5