Sabon dan kwallon da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a kungiyar.
Barcelona ta sayi dan wasan ne daga Borussia Dortmund kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5 domin ya maye gurbin Neymar.
Dan wasan zai isa Spaniya a ranar Lahadi, zai kuma saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, bayan an duba lafiyarsa, sannan a gabatar da shi a gaban magoya baya da 'yan jarida a ranar Litinin.
Dembele shi ne dan wasa na hudu da Barcelona ta saya a bana da suka hada da Paulinho da Nelson Semedo da kuma Gerard Deulofeu.
A cikin watan Agusta ne Neyma ya koma Paris St Germain kan kudi fam miliyan 200, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihi a fagen tamaula a bana.
Neymar ya ci kwallo uku a wasa biyu da ya buga wa PSG a gasar cin kofin Faransa ta bana.
Source: BBC Hausa
Title :
Barcelona Tabaiwa Dembele Rigan Neymar
Description : Sabon dan kwallon da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a kung...
Rating :
5