Barcelona ta kammala daukar Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 96.8 daga baya zai kai fam miliyan 135.5 idan aka hada da tsarebe-tsarabe.
Dan wasan mai shekara 20 dan kwallon Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Nou Camp a gaban shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu a ranar Litinin.
Dembele shi ne na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain daga Barcelona kan fam miliyan 200.
Barcelona ta ce ta gindaya kudi fam miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son sayen dan kwallon idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Nou Camp.
Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barcelona.
Source: BBC Hausa
Title :
Barcelona Ta Kammala Sayan Dembele
Description : Barcelona ta kammala daukar Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 96.8 daga baya zai kai fam miliyan 135.5 idan aka ha...
Rating :
5