Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da shi saniyar-ware ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.
Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buharin ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan da wata jarida ta ce tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga jinya wasu daga cikin 'yan fadarsa da suka yi baba-kere sun ware Farfesa Osinbajo inda ba a damawa da shi a harkokin gwamnati.
"Wannan magana karya ce da jita-jita, maganganu ne marasa tushe da ake kirkiro don ganin an shiga tsakanin wadannan shugabanni masu kwazo," in ji sanarwar.
"Wannan maganar ba abar kamawa ba ce, a ce daga dawowar shugaban kasar cikin mako guda har an fara batun ware mataimakinsa cikin harkokin mulki.
"Abin da nake so a sani shi ne, shi Mr Osinbajo shi ne mutum na kut-da-kut ga shugaban kuma mashawarcinsa na musamman."
Malam Garba Shehu ya kara da cewa, cikin mako guda da ya gabata bayan dawowar Shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo ya halarci tarurruka daban-daban a madadin shugaban, 'in ban da sallar Juma'a.'
Ya kuma yi nuni da cewar masu yada wannan kalamai na karya suna danganta batun ne da cewa Shugaban Ma'aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, shi ne yake yin ruwa da tsaki wajen gabatar da al'amura a fadar, da kuma kin shigar da Farfesa Osinbajo cikin al'amuran gwamnati.
"Babu wani shugaban ma'aikata ciki kuwa har da shi Abba Kyari, da zai aikata irin wannan abu sannan kuma ya ci gaba da kasancewa kan kujerarsa. Wannan mukami ba ya bukatar yada irin wadannan karairayin," in ji Garba Shehu.
Ya kara da cewa a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya a London, ya bai wa Mr Osinbajo goyon baya sosai, "don kuwa ya san maigidansa Shugaba Buhari ba zai so wani abu mara dadi ya faru ba."
"Ni ina ganin Abba Kyari na samun matsala da mutane ne saboda yana son ubangidansa sosai, ba zai dinga bai wa mutane kudi kawai don ya faranta musu rai ba.
"A takaice ma Abba Kyari kudi ba sa gabansa, don ya ki karbar naira miliyan 200 da ake bai wa ofishinsa duk wata don tafiyar da al'amura. Don yana ganin ba a bukatar wannan makudan kudin don tafiyar da al'amuran ofishin nasa," a cewar Garba Shehu.
Dama dai ko a karon farko da SHugaba Buhari ya tafi jinya Birtaniya, an sha yada maganganu irin wadannan da ke cewa wasu 'yan fadar shugaban kasar ba goyon bayan mataimakin shugaban, yayin da wasu kuma ke cewa suna hakan ne don Mr Osinbajon ya fi Shugaba Buhari iya rike mulkin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Ban Maida Obasanjo Saniyar Ware ba-Buhari
Description : Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da s...
Rating :
5