A kasar Saliyo, a kan samu Hausawa a Freetown da Boh da wasu lardunan kasar, wadanda suka shafe shekaru da dama a can suna sana`o`I daban-daban, ciki har da harkar lu`ulu`u ko Daiman.
Wasu daga cikin `ya`ya da jikokinsu ma yanzu ba sa jin harshen Hausa.
Kuma kowane dattijo ka taba, ba ka rasa labarin dalilin da ya tilsta masa barin gida.
Sheikh Muhammad Bello, shi ne babban limamin `yan Najeriya mazauna birnin Freetown, kuma tsohon dan jam`iyyar NEPU ne a Najeriya, ya shaidawa BBC cewa, bacin rai ne ya sa ya bar kasarsa ya koma Saliyo da zama.
Ya ce bayan zaben da aka yi a shekarar 1959, an yiwa jam'iyyarsu mugun kayi, daga nan sai aka fara kuntata musu, aka kuma kafa musu dokoki dan kawai a hana su taro da walwala.
Sheikh Bello ya ce an ci mutuncinsu matuka gaya saboda kawai suna jam'iyyar NEPU.
To wannan dalili ne ya ga ukubar ta yi yawa, shi ya sa ya yi hijira zuwa Saliyo, inda yanzu haka ya ke tare da iyalansa, kuma ya shafe shekaru masu yawa yana zaune a can.
Source: BBC Hausa
Title :
Bacin Raine Ya Tilasta Mini Komawa Saliyo
Description : A kasar Saliyo, a kan samu Hausawa a Freetown da Boh da wasu lardunan kasar, wadanda suka shafe shekaru da dama a can suna sana`o`I daban-da...
Rating :
5