Jamíyyar APC na tsananin sanya wahala da radadi ga mutanen jihar Kogi da Najeriya, cewar wani mamba dake wakiltan yankin mazabar Yagba na jihar Kogi.
Hon Sunday Karimi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, inda ya kaddamar da cewa APC bata cancanci ci gaaba da mulki a jihar ba a 2019.
Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Karimi ya bukacin gwamnan jihar Borno Yahaya Bello day a shirya barin gidan gwamnati kamar yadda zasu kayar da shi.
Dan majalisar yace mutanen da ke fama da kangin talauci sun shirya fitar das hi daga mulki a 2019.
A cewar sa, irin wahala dake ciki jihar ya sa mutane sun zama mabarata sannan kuma hakan ya zamo abun damuwa ga masu kishin jihar.
Ya yi ikirarin cewa jamíyyar PDP zata kwace mulki a 2019, domin maáikata ma na cikin wani hali a jihar.
Title :
APC sun maida ýan Najeriya mabarata – Inji wani dan majalisa
Description : Jamíyyar APC na tsananin sanya wahala da radadi ga mutanen jihar Kogi da Najeriya, cewar wani mamba dake wakiltan yankin mazabar Yagba na ji...
Rating :
5