Gwamnatin Najeriya ta sako ma’aikatan kamfanin hako ma’adinai ‘Solid Unit Limited’ wanda ta kama ranar 14 ga watan Agusta da laifin hako ma’adanai ba tare da izinin yin hakan ba a jihar Filato.
An kama ma’aikatan wanda ya hada da ‘yan kasan Sin 8 da wasu ‘yan Najeriya 12 bayan ziyarar da mai ba shugaban kasa Shawara akan harkar tsaro Ali Monguno da ministan ma’adanai Kayode Fayemi suka kai wuraren da ake hako ma’adanai a jihar.
Mai magana da yawun kamfanin Suleiman Adamu ya fada wa gidan jaridan PREMIUM TIMES a hiran da suka yi ta wayan tarho cewa gwamnatin tarayya ta sako ma’aikatan tun makon da ya gabata amma suna ziyartan shelkwatan ‘yan sanda a Abuja kowani mako sannan za su ci gaba da hakan har na tsawon makonni biyu masu zuwa.
Bayan haka Suleiman Adamu ya zargi mazauna kauyen Bashar dake cikin karamar hukumar Wase a jihar Filato da yi wa kamfanin su cinne bayan sun kammala yarjejeniyyar da kamfanin.
Ya ce dalilin hakan ne ya sa gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Jos ta dakatar da aikin hako ma’adinan sannan hakan ya yi sanadiyyar kama wasu ma’aikatan su a wancan lokacin.
Source: Premium Hausa
Title :
Ansako Ma'aikatan Hako Ma'adanai Da Aka kama A Jihar Filato
Description : Gwamnatin Najeriya ta sako ma’aikatan kamfanin hako ma’adinai ‘Solid Unit Limited’ wanda ta kama ranar 14 ga watan Agusta da laifin hako ma’...
Rating :
5