Wata tsohuwa 'yar kasar Canada ta tsinci tsohon zobenta na zinare a jikin wani karas bayan shekara 13 da bacewarsa.
Tsohuwar mai suna Mary Grams, mai shekara 84, ta yi matukar damuwa da bacewar zoben nata a lokacin da take shuka a lambunta a garin a Alberta shekarar 2004.
To sai dai ta ki bayyana wa kowa labarin batan zoben nata, fiye da shekara 10, sai danta kawai.
A kwanakin baya ne surikar tsohuwar ta ji labarin bacewar zoben bayan da ta ganshi a jikin wani karas
Karas din dai ya fito ne ta tsakiyar zoben, inda ya hakan ya bai wa zoben damar fitowa daga kasa bayan shafe shekaru a boye cikin kasa.
Ta ki bayyayanawa mijinta batan zoben saboda tsoron kada ya yi mata fada, amma kuma ta gaya wa danta.
Ta je kasuwa ta sayo wani zoben makamancinsa, wanda kuma bai kai shi daraja ba, inda ta sanya shi a yatsarta kamar ba abin da ya faru.
"Za a iya cewa na yi ba daidai ba, amma hakan ne mafita kawai," in ji matar.
Babu wanda ya san abin da ya faru, har sai wannan makon lokacin da surikarta Colleen Daley ta ce tana bukatar karas dpn yin abincin dare.
Mis Daley, wacce yanzu ke zaune a gonar da Misis Grams ke zama a baya, ta je gidan gonar ne don debo kayan marmari. Ta gano zoben ne yayin da take wanke karas din da ta debo.
Daga nan sai mijinta wanda daman tuni ya san labarin zoben, ya yi sauri ya kira mahaifiyar tasa.
Yayin da take tuna baya, Misis Grams ta ce ta yi da-na-sanin rashin fada wa mijinta wanda ya rasu shekara biyar da suka wuce, gaskiyar abin da ya faru.
Ta ce mutum ne mai raha, wanda ko da yaushe ke cikin yanayi na raha da farin ciki. Yanzu da ta samu zoben nata, ta ce za ta kara kula da shi sosai.
"Duk lokacin da zan fita, ko zan je wani wuri zan rika boye shi a wuri na musamman. Wannan shi ne abin da zan rika yi," in ji ta.
Wannan ba shi ne karo na farko ba aka taba tsintar zoben zinare a jikin karas ba. A shekarar 2011, wata mata 'yar kasar Sweden ta tsinci zoben aurenta bayan shekara 16 da bacewarsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Angano Wani Zoben Zinaren Da ya Bata Ajikin Wani Karas Bayan Shekara 13
Description : Wata tsohuwa 'yar kasar Canada ta tsinci tsohon zobenta na zinare a jikin wani karas bayan shekara 13 da bacewarsa. Tsohuwar mai suna M...
Rating :
5