Shugaban rundunar tsaro na NSCDC reshen jihar Sokoto, Babangida Dutsin-Ma ya ce hukumarsa ta gano wata boyayyiyar matatar man fetir a jihar Sokoto.
Ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillanci labaran Najeriya ranar Juma’a a garin Sokoto.
Bayanan bincken da hukumar ta yi sun nuna cewa wani sanannan dan kasuwa ne mai mallakin matatar man da yake wani gida dake hanyar zuwa Bodinga.
Babangida Dutsin-Ma ya ce ma’aikatan sun hada wutan lantarkin da suke amfani da shi a matatar ta hanyar wata tiransifoma da suka boye a wata katotuwar rami.
Ya ce matatar na sarafa man fetir, kalanzir da sauransu.
Ma’aikatan matatar sun gudu lokacin da jami’an NSCDC suka iso wurin amma sun kama wasu kayayyakin da suke aiki da su da ya hada da wayoyin wutan lantarki, galoli da sauransu.
Source: premium Hausa
Title :
Angano Wani Matatar Mai A Sokoto
Description : Shugaban rundunar tsaro na NSCDC reshen jihar Sokoto, Babangida Dutsin-Ma ya ce hukumarsa ta gano wata boyayyiyar matatar man fetir a jihar ...
Rating :
5