Fadar Shugaban Najeriya ta ce nan gaba a yau Asabar ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida bayan wata doguwar jinya a birnin Landan.
A cikin wata sanarwa da Mai bai wa shugaban Shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar ya ce ana sa ran shugaban ya yi wa 'yan kasar jawabi ta gidajen radiyo da tallabijin ranar Litinin da safe.
''Ya gode wa daukacin 'yan Nigeria wadanda suka yi ta yi masa addu'ar samun lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara jinya,'' inji takaitacciyar sanarwar mai sakin layi hudu.
Source: BBC Hausa
Title :
Anasa Ran Buhari Zai Dawo Nigeria Yau
Description : Fadar Shugaban Najeriya ta ce nan gaba a yau Asabar ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida bayan wata doguwar jinya a birnin L...
Rating :
5