Mahukunta a Saliyo sun umarci mazauna yankin Regent, unguwar da masifar zabtarewar kasar ta halaka daruruwan jama`a da su kaura zuwa wani wuri saboda yankin na fuskantar yiwuwar sake zabtarewar kasa a nan gaba.
An dai yi jana`izar akalla mutum 550, wandanda masifar zabtarewar kasa da ambaliya suka halaka, yayin da alkaluma ke cewa har yanzu ba a ji duriyar wasu mutum 600 ba.
Hukumar kula da al`amuran da suka shafi bala`i a kasar ta ce tun aukuwar masifar ta dukufa wajen gano musabbabin hadarin da hanyoyin kare aukuwarsa gaba; kuma ta gano ya zama dole mutanen gangaren su kaura.
Source: BBC Hausa
Title :
An Umurci Masu Makwabta Da Tsauni Dasu Kaura-Saliyo
Description : Mahukunta a Saliyo sun umarci mazauna yankin Regent, unguwar da masifar zabtarewar kasar ta halaka daruruwan jama`a da su kaura zuwa wani wu...
Rating :
5