Rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya, Abuja, ta kori 'yan sanda hudu da ake zargi da hannu a wawushe wani gidan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, da ke unguwar Gwarimpa a Abuja.
Wata sanarwar da rundunar ta fitar ta ce bayan an gudanar da bincike kuma an samu 'yan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasan da hannu cikin satar da aka yi a gidan, kwamishinan 'yan sandan birnin, CP Musa Kimo, ya amince da korar 'yan sandan hudu.
Wadanda aka kora din sun hada da Sajen Musa Musa da Sajen John Nanpak da Sajen Ogah Audu da kuma Sajen Gabriel Ugah.
Har wa yau an mika sunayen Sufeto Lengs Satlakau da kuma Sufeto Usman Wuduki ga matamaikin Sufeto Janar da ke kula shiyya ta bakwai domin daukar mataki.
Rundunar ta kara da cewa, za ta gurfanar da wanda aka fi zargi da aikata laifukan, Sajan Musa Musa, a gaban kuliya yayin da take kokarin kamo Mallam Shuaibu da ake zargin ya taimaka masa wajen aikata laifin.
A ranar Larabar da ta gabata ne mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya fidda sanarwar cewa a watan da ya gabata barayi suka shiga gidan Goodluck Jonathan, da ke unguwar Gwarimpa suka wawushe duk wani abu da hannu zai iya fitarwa a gidan.
Sai dai mai magana da yawun Mista Jonathan din ya ce, wasu kafofin yada labaran sun zuzuta yawan kayan da aka sace din, inda suke cewa an sace talbijin 36 da firinji 25.
"Abubuwan da aka sace sun hada da talbijin shida da firinji uku da kuma na'urar dafa abinci guda daya," a cewarsa.
BBC Hausa
Title :
An Kori Ya Sanda Da Sukayi Sata A Gidan Goodluck Jonathan
Description : Rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya, Abuja, ta kori 'yan sanda hudu da ake zargi da hannu a wawushe wani gidan tsohon shugab...
Rating :
5