Kimanin 'yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da na 'yan kasa da shekara 21.
'Yan wasan da za su buga wa kasashensu fafatawar shiga gasar kofin duniya sun hada da Marco Asensio da Dani Carvajal da Isco da Nacho da Sergio Ramos da Lucas Vazquez.
Sauran sun hada da Cristiano Ronaldo da Luka Modric da Mateo Kovacic da Keylor Navas da Gareth Bale da Casemiro da Marcelo da Toni Kroos da kuma Achraf.
Su kuwa Borja Mayoral da Dani Ceballos za su buga wa Spaniya wasan matasa 'yan kasa da shekara 21 na sada zumunta da Italiya da na neman shiga gasar Zakarun Turai da Estonia.
Real Madrid za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na uku a gasar La Liga a ranar 9 ga watan Satumba, kwanaki hudu tsakanin ta buga wasan gasar cin kofin Zakarun Turai da Apoel Nicosia a Santiago Bernabeu.
Source: BBC Hausa
Title :
An Gayyaci Yan Madrid Sha Bakwai Tawagan Kasashensu
Description : Kimanin 'yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da...
Rating :
5