Mutane 16 sun mutu daga watan Yuni zuwa yanzu sanadiyar ambariyar ruwan sama a birin Yamai na jumhuriyar Nijar.
Hukumomin kasar sun yi kira ga jama'ar da ke zaune a kewayen wuraren da ruwan sama ke wa barazana da su gaggauta barin gidajensu.
Ruwan saman da ake yi kamar da bakin kwarya, ya sa an samu mummunar ambaliya a wasu unguwani na birnin, ganin cewa jama'a sun yi gine-gine a kan tsoffin magudanan ruwa.
Bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin na Yamai, wadanda masana kimiyya suka kiyasta cewa, yawan ruwan ya haura milimita 100 , kwatankwacin sama da inci 4, kuma ruwan ya zuba ne a cikin sa'o'i kalilan.
Hakan ne ya hadasa ambaliyar da ta yi sanadiyar faduwar wasu gidaje a ranar Asabar a wasu shiyoyi na birnin Yamai, inda har wani magidanci da dan sa suka rasa ransu.
A yanzu haka gidaje da dama da aka gina a kan tsofaffin magudanan ruwa a wasu unguwani kamar Guntu Yena, da suke bakin kwazazaben kogin kwara wato gulbin Isa -Fleuve Niger, sun cika makil da ruwa, inda su ke fuskantar hadarin faduwa.
Ruwan saman ya yi sanadiyyar rusa da gidaje sama da 300 tare da jikkata mutane da dama a kauyen Gabagura da ke yammacin birnin na Yamai.
Yanzu haka mutane da dama na fakewa wa ne a cikin azuzuwan wasu makarantun boko.
Tuni dai mahukunta a birnin na Yamai, su ka yi kira da babbar murya ga wadanda ke zaune har yanzu a wuraren da ke fuskantar ambaliyar da su tattara na su ya na su su bar wuraren.
Rahotanni sun sanar da cewa tun farkon damunar bana zuwa yanzu, adadin mutanen da suka mutu a hukumance, sanadiyar ambaliyar ruwa a fadin kasar ta Nijar , sun kai mutun 41, kuma sama da 68, 000 ne lamarin ambaliyar ya shafa.
A bara kuma a dai-dai wannan lokaci, ambaliyar ta kashe mutum 50, tare da tagayyarar wasu 145, 000, musaman a yankin Tahaoua da Agadez, duk da cewa yankunane na hamada masu kekasashshen yanayi.
Source: BBC Hausa
Title :
Ambaliyar Ruwa Yayi Barna A Niger
Description : Mutane 16 sun mutu daga watan Yuni zuwa yanzu sanadiyar ambariyar ruwan sama a birin Yamai na jumhuriyar Nijar. Hukumomin kasar sun yi kira...
Rating :
5